Kada barazanar matasan Arewa ya tsorataku, ku zauna daram dam a Sokoto abinku - Tambuwal ga ‘yan kabilar Igbo

Kada barazanar matasan Arewa ya tsorataku, ku zauna daram dam a Sokoto abinku - Tambuwal ga ‘yan kabilar Igbo

- Gwamnan jihar Sokoto ya yi kira ga al’umman Igbo dake zaune a jihar sa da su shirya ci gaba da zama a jihar

- Ya ce suma suna da hakki a jihar kamar ko wani dan Najeriya

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga al’umman Igbo dake zaune a jihar sa da su shirya ci gaba da zama a jihar saboda Sokoto gidan kowani dan Najeriya ne suma gida ne a wajen su.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a wajen wani taron bude baki da ya yi da ‘yan Kabilar Igbo mazauna jihar sa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Kada barazanar matasan Arewa ya tsorataku, ku zauna daram dam a Sokoto abinku- Tambuwal ga ‘yan kabilar Igbo

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga al’umman Igbo dake zaune a jihar sa da su shirya ci gaba da zama a jihar saboda Sokoto gidan kowani dan Najeriya ne

Ya kara da cewa yana tare da shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kan raddin da suka maida wa matasan Arewa da suka bukaci ‘yan kabilar Igbo su koma yankinsu tunda sunce su Biyafara suke so.

”Kada wani dan Kabilar Igbo ya ta da hankalisa musamman idan mazaunin Sokoto ne domin babu wani da ya Isa ya taba lafiyarsa.”

Shugaban tawagar Igbo din ya shaida wa gwamnan cewa basu taba samun wata fargaba ba a tsawon zamansu a jihar. Sun kuma godewa Tambuwal da bude baki da ya gaiyace su.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel