Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram sun kammala mummunan harin da suka kai babban birnin jihar Borno, Maiduguri, a wannan shekara ta hanayar sakin sabon biyo na farfaganda.

An saki bidiyon wanda ya nuna hare-hare da aka kai tsakanin ranar Laraba da Alhamis (7-8 ga watan Yuni) ga gidajen jaridu a karshen wannan mako

1. Har yanzu kungiyar Boko Haram na da isasun manyan motoci tare da muggan makamai daure a kan su

Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Wayoyin sadarwa da kungiyar suka samu

A cikin bidiyon an gano manyan motoci na yaki da daban-daban. Dukkanababen hawan na dauke da na’aurar bindigogi daban-daban.

Har ila yau, irin wannan tarin motoci na bukatar a dunga zuba masu mai. Hakan na nufin cewa har yanzu kungiyar na da masu yi masu safarar man fetur.

2. Masu kare Maiduguri sun gina manyan ramuka domin hana motoci kai hari birnin

Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Mutanen Maiduguri sun gina manyan ramuka domin hana motoci kai hari birnin

An lalata wasu hanyoyi dake sada mutun da birnin da gangan. Mayakan Boko Haram sun dauki shebur da hannayensu sannan kuma sun gina gadoji don ci gaba da kai mamayarsu.

3. Yan Boko Haram sun lalata tashar bincike na sojoji

Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Yan Boko Haram sun lalata tashar bincike na sojoji bayan daya daga cikin hare-haren su

Bidiyon ya nuna cewa ‘yan Boko Haram sun yi nasarar farfadowa. Makamai, kayayyakin aiki da kuma wasu abubuwa da suke amfani da shi gurin kai mummunan harin su. Ba’a san makomar sojojin dake kare yankin ba.

4. Bidiyon Boko Haram ya nuna kayayyakin da suka samo da kuma cikekken bayanan su

Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Daga cikin kayayyakin da suka samo

Kungiyar ta’addan sun samu bindigogi, bama-bamai, magunguna da ko wani irin magani. Wani dan ta’adda ba ba’a nuna fuskar sa ba, ya yi magana game da nasaran a kamara na kusan mintuna bakwai.

Ya sanya kayan sojoji sannan kuma sanye yake da sabon takalmin soja. Akwai yiwuwar ya same su ne ‘yan mintoci kadan daga wanda ke kare tashar binciken da suka kama.

5. A yanzu yan ta’addan na da kayan sadarwa da dama

Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

'Yan ta'addan sun nuna kayayyakin sojoji da suka samo a bidiyon

Bidiyan farfagandan ya nuna yan ta’addan Boko Haram suna da wayoyi da kuma kayan sadarwa na radiyo da dama a yanzu.

6. An nuno takardu, adabi da kuma kayayyakin sojoji

Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Makamai da yan kungiyar suka baza

Bidiyon Boko Haram ya kuma nuno wasu takardu da aka samo daga tashar binciken. A halin da ake ciki, yan ta’addan basu gabatar da wani tikitin shaida na ko wani soja ko kuma wasu takardu masu muhimmanci ba.

Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Takalmin sojoji

A yanzu yan ta’addan na da tarin kayan sojoji da takalman su.

7. Dajin Sambisa na karkashin kulawa, amma Abubakar Shekau yay i fushi fiye da da sannan kuma ya fi da hatsari

Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Motocin 'yan ta'addan

Ko da ace Shekau na ainahi yam utu, magajin sa na nan lafiya. Har yanzu kungiyar na da mayaka isassu, ya kamata a lalata sababbin motocin dake a bayan bindiyon. Da zafi-zafi a kan bugi dutse.

NAIJ.com na ganin cewa, dukkan wadannan sun isa dalilan da zasu sa hukumar soji da duk wani kungiyar doka su kara kaimin tsaron su.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel