Shekau ya fito a sabon BIDIYO, ya yi ikirarin nasara a harin Maiduguri

Shekau ya fito a sabon BIDIYO, ya yi ikirarin nasara a harin Maiduguri

- Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya saki sabon bidiyo a kan hare-haren Maiduguri

- Ya ce suna ci gaba da samun nasara, tare da karyata cewan an kashe wasu mutanen sa

- Shekau ya ce bazasu daina kai hari ba indai za’a ci gaba da ilimin Boko da tsarin mulkin demokradiyya

- Daga karshe ya ce azumin banza ‘yan Maiduguri ke yi tunda baza bin koyarwar addini yadda ya kamata

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya saki sabon bidiyo inda yake murnan nasara da suka samu kan harin ta’addanci da suka kai Maiduguri sannan kuma ya sha alwashin cewa hare-haren zai ci gaba har sai an cika ka’idojin sa.

NAIJ.com ta rahoto cewa akwai hare-hare da aka shirya a babban birnin Borno ko da dai hukumar soji ta yi ikirarin cewa ta dakile harin sannan kuma cewa an kashe yan ta’addan uku.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa wasu yan Najeriya ke son shugaba Buhari ya mutu – Fadar shugaban kasa

A cikin sabon bidiyon, Shugaban kungiyar ta’addan ya karyata cewan an kashe mutanen sa, ya nace kan cewa lallai su nasara suka yi.

A cikin bidiyon mai tsawon mintina 23, Shekau wanda ya yi magana a harshen Hausa yak e ilimin Boko da tsarin mulkin damokradiyya sabo ne sannan kuma ya ce idan har za’a ci gaba da amfani da su, lallai hare-haren zasu ci gaba.

“Nine Abubakar Shekau, shugaban kungiyar da aka fi sani da Jamaatu Ahlil Sunna Li Dawati wal Jihad. Muna godiya ga Allah da ya kawo mu wannan rana.

“Muna farin ciki sannan kuma muna jinjina ga ‘yan uwanmu da aka baza a fadin duniya kan cewa Allah ya bamu nasara bayan Ya kai mu birnin Maiduguri, inda Allah ya taimake mu muka kori kafiran sojoji sannan kuma ya bamu nasara a kan su.

“Sojojin na nan suna farautarmu a dajin Sambisa, amma mu gamu muna kai masu yaki a cikin gari. Mun zo birnin Maiduguri sannan kuma sojoji sun ganmu sun tsere.

"Sun kuma yi karyan cewa sun kashe mu. Amma wannan ba gaskiya bane. Babu abun da ya faru da mayakan mu.

"Munje gurin kuma Allah ya taimake mu mun kori kafiran. Ba yin mu bane, amma na Allah. Munje Maiduguri sannan mun kashe wadanda suka cancanci mutfuwa sannan kuma Allah ya taimaka mana gurin kashe su."

Kalli cikakken jawabin sa a cikin bidiyon a kasa:

Ya kuma bayyana wa mazauna Maiduguri cewa azumin su a banza ne tunda ba sa aiki da koyarwan addini kamar yadda ya kamata.

NAIJ.com ta kawo maku bidyon yadda rundunar sojin Najeriya ke yakar Kungiyar Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras
NAIJ.com
Mailfire view pixel