An dakatar da 'yar jaridar da ta fadi mutuwar shugaban kasar Gabon

An dakatar da 'yar jaridar da ta fadi mutuwar shugaban kasar Gabon

- Kasar Gabon ta dakatar da wata ‘yar jarida dake aiki gidan tralbijin

- An dakatar da ita ne bayan ta yi kuskure gurin cewa shugaban kasar Ali Bongo ya rasu

- Ta yi subutan baki ne wajen cewa mahaifin shugaban kasar Omor Bongo ya rasu shekarun baya

Hukumomi a kasar Gabon sun dakatar da wata yar jarida dake gabatar da labarai a gidan talabijin sakamakon kuskure da ta yi wajen cewa shugaban kasar Ali Bongo ya rasu.

Wivine Ovandong, ta so ne ta ce mahaifin shugaban kasar, wato marigayi Omar Bongo, ya mutu shekara takwas da suka wuce - da yake ana jimanin tunawa da mutuwar tasa.

KU KARANTA KUMA: Zagon kasa: Sanatoci sun hana Gwamnatin Buhari aikin titin jirgin kasa

An dakatar da 'yar jaridar da ta fadi mutuwar shugaban kasar Gabon

Omar Bongo ya kwashe fiye da shekara 40 a kan mulki

Mr Bongo ya kwashe fiye da shekara 40 a kan mulki.

Ya mutu ne a shekarar 2009 kuma ɗansa Ali Bongo ne ya gaje shi.

Ms Ovandong ta soma aikin gabatar da labarai ne kwanaki kadan da suka wuce, ko da yake a baya tana aiko da rahotanni.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda Jama'a ke zama a Garin Ohuhu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel