Zagon kasa: Sanatoci sun hana Gwamnatin Buhari aikin titin jirgin kasa

Zagon kasa: Sanatoci sun hana Gwamnatin Buhari aikin titin jirgin kasa

– Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya zargi Majalisa wajen hana aikin jirgin kasa

– Sanatoci sun hana a aro kudin da ake bukata wajen wannan kwangila

– Ana dai takon-saka tsakanin Gwamnatin Shugaba Buhari da Majalisa

Har yanzu Majalisa ba tayi na’am da rokon Gwamnati na karbo bashi ba

Ministan sufuri na kasa yace wannan ya hana a cigaba da aiki

Rotimi Amaechi ya zargi Majalisa da hana a karbi aron makudan kudi daga China

Rotimi Amaechi

Ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi

KU KARANTA: Osinbajo ya halarci wani daurin auren jigon APC

Ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi yace Majalisar Dattawa ta hana a cigaba da aikin jirgin kasa wanda zai ci sama da Dala Miliyan 5.8. Amaechi yace Sanatoci su ka hana a karbi aron wannan makudan kudi daga kasar China.

Zagon kasa: Sanatoci sun hana Gwamnatin Buhari aikin titin jirgin kasa

Ministan sufuri na kasa yace rashin kudi ya hana a cigaba da aiki

Amaechi ya kuma musanya zargin cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta kebe Yankin kudu maso gabashin kasar wajen bada ayyuka yace sam wannan ba gaskiya bane. Ana dai shirin aikin jirgin kasa daga Garin Legas zuwa Kalaba.

Kwanan nan mu ke ji daga Hukumar NEITI mai bin diddiki cewa Dala Miliyan 36.9 yayi dabo a Najeriya a lokacin mulkin Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan. Wannan kudi dai na man kasar ne da aka saida.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda Jama'a ke zama a Garin Ohuhu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel