Najeriya na shirin fara fitar da doya zuwa sasashen Turai

Najeriya na shirin fara fitar da doya zuwa sasashen Turai

Ministan kula da harkokin Noma da cigaban karkara, Cif Audu Ogbeh ya bayyana cewa, Nijeriya na shirinta na farko na fitar da zababbun doya zuwa kasasshen Amurka da Birtaniya a cikin wannan watan na Yuni.

Wannan shiri, gwamnati na fata zai kawo ci gaba ga al’amuran tattalin arziki da kuma habaka harkokin noma a Nijeriya.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a wata sanarwa da mataimaki na musamman akan harkokin yada labarai na ministan, Dakta Kayode Oyeleye ya fitar, ya bayyana cewa akwai tsare-tsare da dama da gwamnati ke yi na ganin cewar shirin fitar da abubuwa daga Nijeriya zuwa kasashen duniya ya yi nasara.

Najeriya na shirin fara fitar da doya zuwa sasashen Turai

Najeriya na shirin fara fitar da doya zuwa sasashen Turai

A cewarsa, Hukumar Alkinta Amfanin Gona ta Kasa ta dau aniyar tabbatar da cewa masu sana’ar fitar da kayan amfanin gona zuwa kasashen ketare sun cika ka’idar fitar da amfani ingantacce don gudun jawowa kasar abin kunya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel