Biafra : Babu wanda ya isa ya rainawa Arewa wayo - Junaid Mohammed

Biafra : Babu wanda ya isa ya rainawa Arewa wayo - Junaid Mohammed

Tsohon dan majalisa, Dakta Junaid Mohammed yayi gargadi ga yan kabilan Igbo da su daina amfani da Biafra wajen barazana ga 'yan Najeriya.

Junaid wanda yayi wannan gargadi yayi kira da gwamnatin tarayya ta hana shugabannin Inyamurai amfani da yakin neman Biafra wajen addaban jama’an Najeriya.

Yayinda yake magana da jaridan vanguard, Mohammed yace : “Shin ta wani dalili dattawan arewa zasu goyi bayan shirin koran yan kabilan Igbo daga Arewa? Su kuma Igbo su sani cewa basu kadai suka iya rikici ba kuma basu fi sauran yan Najeriya ba ta ko wani hanya da zasu dinga barazana kan mutane.”

Biafra : Babu wanda ya isa ya rainawa Arewa wayo - Junaid Mohammed

Biafra : Babu wanda ya isa ya rainawa Arewa wayo - Junaid Mohammed

“Wadanda ke daukan nauyin wannan yaudararren yakin neman Biafra suna yawo a titi kuma babu wanda yake wani magana akai. abin takaici ne gwamnatin Buhari ta bari yakin neman Biafra ya damu kasa.

KU KARANTA: ISIS tayi barazanan kai hari kasar Saudiyya

“Wannan babban barazana ne ga Najeriya wanda Igbo suka shirya kuma bai dace gwamnati tu tsira ido ba saboda wasu dalilai na siyasa.”

“Idan gwamnatin Buhari ta cigaba da barinsu suna yakin neman Biafra inda suka gargadi ga matasan Arewa, za’a samu matsala saboda babu wanda zai iya rainawa arewa wayo.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel