Kungiyar ISIS tayi barazanar kai hari kasar Saudiyya

Kungiyar ISIS tayi barazanar kai hari kasar Saudiyya

Kungiyar ISIS tayi barazanar kai hari kasar Saudiyya bayan ta dau alhakin harin kasar Iran inda rayuka 17 suka hallaka.

A ranan Laraba, 7 ga watan Yuni, yan kunar bakin wake sun kai hari majalisar dokokin kasar Iran da kabarin Ayatollah Khomeini.

Kungiyar ISIS ta dau alhakin kai wannan hari kuma tayi barazanar cigaba da kai ire-iren irin wannan hari.

A wata bidiyo da ta saki kafin kai hari, an gay an kungiyar 5 fuska a rufe suna barazana ga yan Shia a Iran kuma sunce lokacin kasar Saudiyya na zuwa.

Kungiyar ISIS tayi barazanar kai hari kasar Saudiyya

Kungiyar ISIS tayi barazanar kai hari kasar Saudiyya

Yace: “Ku sani cewa bayan kasar Iran, saura ku. da ikon ubangiji zamu kai muke hari gidajenku….Muna yaki ga addinin Allah ne ba kasar Iran ba ko kasar larabawa ba.”

Kungiyar ISIS wacce ta kwace wasu yankuna a kasar Syria da Iraqi ta kai hare-hare ga rundunar kasar Saudi, kana kuma suna kai hare-hare wurare daban-daban.

KU KARANTA: Saura kiris almajiri ya hallaka

An kasance ana samun tashi hankali a yankin larubawa tun lokacinda kasar Saudiyya, Misra Dubai,da Bahrain suka yanke hulda da kasar Qatar bisa ga zargin taimakawa ta’addanci.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel