An sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Kaduna

An sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Kaduna

- Rahotanni sun kawo cewa anyi nasarar karboi wasu daga cikin mutanen da akayi garkuwa da su a hanayar Kaduna zuwa Abukja

- Wani mazaunin jihar Kaduna mai suna Kwamared Danjuma Sarki ya tabbatar da hakan

- A cewar sa an saki mutane uku ne bayan an biya kudin fansar su

- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta musanta sace mutum 20 a hanyar Abuja

An karbo uku daga cikin mutane ashirin (20) da aka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja

A cewar hukumar BBC Hausa, wani dan asalin jihar Kaduna mai suna Kwamared Danjuma Sarki, wanda ya wallafa sace wasu abokansa a shafukan sada zumunta ya bayyana cewa an karbo mutanen ne bayan an biya kudin fansar su.

''Sun bukaci kudin fansa, na kuma kai musu; ba su sako sauran mutanen da aka yi garkuwa da su ba, don haka mutum uku kadai suka ba ni'', cewar Danjuma.

An sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Kaduna

An sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Sai dai bai bayyana adadin kudin da ya bayar kafin a saki mutanen ba.

Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta musanta sace mutum 20 a hanyar Abuja.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Aliyu Usman ya bayyana cewa "babu wani rahoto mai makamancin wannan da 'yan uwa ko wasu mazauna yankin suka kai wa jami'an tsaro kamar yadda aka saba a baya".

A cewarsa, mutum biyar kawai suka samu labarin an sace a hanyar.

Jama'a a yankin birnin Gwari na jihar Kaduna ma na ci gaba da zama cikin zilama, saboda sake dawowa da dauki dai-dai din da ake yi musu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel