YANZU YANZU: Yan Boko Haram sun kai mummunan hari a Kamaru

YANZU YANZU: Yan Boko Haram sun kai mummunan hari a Kamaru

- An rahoto cewa ‘yan kunar bakin wake sun kai hare-hare guda hudu cikin sa’o’I 24

- Wani dan kunar bakin wake ya tayar da kansa wanda ya yi sanadiyar mutuwar soja daya

- Al’amarin ya faru ne a matatarar tsaro dake Kolofata

Wani harin bam ya afku a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, a sansanin Kolofata dake kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.

Anyi sa’a harin bai kashe ko wani dan farar hula ba amma dai hasashe sun nuna cewa ta’addancin kungiyar Boko Haram ya fara shafar sauran kasashe.

Abun bakin ciki soja daya yam utu sannan kuma wasu biyu sun ji rauni.

NAIJ.com ta tattaro cewa dan kunar bakin waken ya yi nasarar kutsawa cikin sansanin tsaro a Kolafata sannan ya tayar da kansa.

KU KARANTA KUMA: Wani soja ya bindige wasu mutane uku har lahira a Kaduna

L’Oeil du Sahel, waninjaridar Kamaru, a shafin su na Facebook sun rahoto cewa wannan ne bkaro na hudu da aka kai harin kunar bakin wake cikin sa’o’I 24.

A cewar wani rahoto da NAIJ.com ta kawo a baya, wasu yan ta’addan Boko Haram sun kai hari Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel