Aisha Buhari ta aika sako mai girma ga ‘Yan Najeriya a lokacin Ramadan

Aisha Buhari ta aika sako mai girma ga ‘Yan Najeriya a lokacin Ramadan

- Uwargidan shugaban kasa Buhari ta nuna bukatar hadin kai da zaman lafiya a tsakanin ‘yan Najeriya

- Uwargidan shugaban kasar da sauran manyan masu fada a ji sun yi addu’oi ga maigidanta da kuma kasar

- Ta ce: "yana da matukar muhimmanci mu hade kanmu ta hanyar yada al’ddun mu daban-daban a tsakaninmu

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa kasar addu’o’in hadin kai da zaman lafiya.

Ta yi kiran ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni a shafinta na twitter bayan ta halarci taron addu’o’I da tafsir na Ramadan da ma’aikatan fadar shugaban kasa suka shirya a Abuja.

Aisha Buhari ta ce: “yana da matukar muhimmanci mu hade kanmu ta hanyar yada al’ddun mu daban-daban a tsakaninmu.

Aisha Buhari ta aika sako mai girma ga ‘Yan Najeriya a lokacin Ramadan

Aisha Buhari ta aika sako mai girma ga ‘Yan Najeriya a lokacin Ramadan

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Aisha Buhari ta yi godiya ga 'yan Najeriya kan tarin addu'o'i da fatan alkhairun su ga maigidan ta shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ta kuma ba da tabbacin cewa shugaban kasar na samun sauki sosai kuma zai dawo nan ba da jimawa ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel