Wani soja ya bindige wasu mutane uku har lahira a Kaduna

Wani soja ya bindige wasu mutane uku har lahira a Kaduna

- An shiga tashin hankali a jihar Kaduna bayan rahotannin dake cewa sojoji sun harbe wasu mutane

- An rahoto cewa an zuba jami’an tsaro don su tabbatar da zaman lafiya

An shiga tashin hankali a jihar Kaduna bayan rahotannin dake cewa sojoji sun harbe wasu mutane a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni.

A rahoton da shaidar gani da ido y aba NAIJ.com ya yi ikirarin cewa al’amarin ya afku ne lokacin da wani yaro ya yi yunkurin dibar yashi a wata kwalbati dake kusa da makarantar sakandare na Command.

A cewar rahoton daya daga cikin sojojin ya harbi yaron.

Wani soja ya bindige wasu mutane uku har lahira a Kaduna

Kafa ya dauke a unguwar sakamakon rikicin

Matasa ko da suke kusa da wurin su ka taso wa sojan daga nan ko gogan naka sai ya hau bude wata inda yayi sanadiyyar rayukan wasu matasan biyu kuma.

Da kyar dai aka samu aka tausasa matasan inda shi kuma sojan ya gudu cikin makarantar Command.

Wani soja ya bindige wasu mutane uku har lahira a Kaduna

Wani soja ya bindige wasu mutane uku har lahira a Kaduna

Rundunar Soji a Kaduna ta fitar da rahoton cewa lallai zata binciki al’amarin sannan ta roki matasa da mazauna unguwan da su kwantar da hankalinsu.

Kalli bidiyon NAJ.com kan ayyukan sojoji a kan yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel