YANZU YANZU: ‘Yan bindiga sun sace dan majalisar jihar Kaduna mai shekaru 42 da wasu mutane 3 (HOTUNA)

YANZU YANZU: ‘Yan bindiga sun sace dan majalisar jihar Kaduna mai shekaru 42 da wasu mutane 3 (HOTUNA)

- An sace wani dan majalisar dokokin jihar Kaduna, Isa Salihu

- Dan majalisar mai shekaru 42 na wakiltan mazabar Magajin Garin dake jihar Kaduna

- An sace Salihu tare da wasu mutane uku a hanyar Kaduna-Birnin Gwari

Wasu ‘yan bindiga kimanin su 30 sun yi garkuwa da dan majalisar dokokin jihar Kaduna, Isa Salihu wanda ke wakiltan mazabar Magajin Garin dake jihar, Channels TV ta rahoto.

NAIJ.com ta tattaro cewa an sace dan majalisar mai shekaru 42 tare da wasu mutane uku a hanyar Kaduna-Birnin Gwari.

An sace dan majalisar ne a hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari daga babban birnin jihar.

KU KARANTA KUMA: Kotun soji ta yankewa sojan Najeriya hukuncin kisa akan kisan dan Boko Haram

YANZU YANZU: ‘Yan bindiga sun sace dan majalisar jihar Kaduna mai shekaru 42 da wasu mutane 3 (HOTUNA)

Kimanin ‘Yan bindiga 30 sun sace dan majalisar jihar Kaduna, Isa Salihu

Wata majiya a majalisar dokoki na jihar ta ce ana nan ana kokarin ceto dan majalisar daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

A halin yanzu hukumar yan sanda na jihar basu tabbatar da al’amarin ba tukuna.

NAIJ.com ta rahoto a baya cewa anyi garkuwa da wani dan majalisar jihar Kano mai wakiltan Sumaila/Takai dake jihar Kano, Garba Durbunde a ranar Talata, 30 ga watan Mayu.

An sace sa ne a yayinda yake tuki daga Abuja zuwa Kano.

Wadanda suka yi garkuwan da shi sun sake shi a daren ranar Laraba, 31 ga watan Mayu bayan an biya su kudin fansa.

NAIJ.com ta tattaro maku nasarorin shugaba Buhari a shekaru biyu da ya yi yana mulki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel