Zaben 2019: An kaddamar da gangamin yakin neman zaben Buhari ta 2019 a yammacin Najeriya

Zaben 2019: An kaddamar da gangamin yakin neman zaben Buhari ta 2019 a yammacin Najeriya

- An kaddamar da gangamin farfado da kungiyar yakin neman zaben shugaban kasar Muhammadu Buhari ta 2019 a karon farko

- Kungiyar BCO ta kaddamar da taron ne domin neman wa shugaba Buhari wa'adi na biyu a ofis

- A garin Abeokuta da ke yankin kudu maso yammancin Najerriya ne aka kaddamar da taron

Yankin kudu maso yammancin Najeriya ta kaddamar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasar Muhammadu Buhari ta 2019 a karon farko wato Buhari Campaign Organization (BCO) a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Kungiyar yakin neman zaben shugaba Buhari wanda aka kaddamar domin neman wa shugaba Buhari wa'adi na biyu wanda kuma wa’adinsa na farko zai ƙare a ranar 29 ga Mayu, 2019.

Shugabannin kungiyar BCO daga yankunoni 6 na kasar sun hadu a Abeokuta inda suka kuma gudanar da wani taro wanda zai farfado da kungiyar yakin neman zaben shugaba Buhari a zabe mai zuwa na 2019 a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Zaben 2019: An kaddamar da gangamin yakin neman zaben Buhari ta 2019 a yammacin Najeriya

Shugaba Buhari, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da gwamnan jihar Ekiti a lokacin yakin neman zabe a jihar

KU KARANTA: Aisha Buhari da wasu matan jiga-jigai sun yi wa Buhari da Najeriya addu'a (Hotuna)

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, Shugaban BCO ta kwamitin amintattu na Jam'iyyar, Alhaji Kabiru Dutsin-Ma ya ce sun dauki wannan matakin ne don tabbatar da cewa manufofin Shugaba Muhammadu Buhari ya jimre.

Shugaban ya ci gaba da cewa dole ne su dauki matakan farfado da kungiyar yanzu domin tabbatar da cewa manufofin shugaba Buhari ya jimre da kuma haifar da wayar da kan jama'a a kan gagarumin kokari da nasarorin da shugaba Buhari ya yi a gwamnatin sa.

Mambobin BCO ta kwamitin amintattu na Jam'iyyar da suka halarci taron sun hada da Hassan Isiyaka (Sarki Kudu), Ambasada (Dr). Abdullahi Bawa Wase da Alhaji Salisu Garba (Sarkin Fulani Sagamu), Cif Otetola Tunde tare da wasu sarakunan gargajiya daga Abeokuta da sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani jami'in jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel