Toh fa: Majalisar Dattijan Najeriya ta bukaci wani babban ministan Buhari ya gurfana a gaban ta kan wani kwangila

Toh fa: Majalisar Dattijan Najeriya ta bukaci wani babban ministan Buhari ya gurfana a gaban ta kan wani kwangila

- Majalisar dattijan Najeriya ta bukaci ministan makamashi, ayyuka da gidaje ya gurfana gaban kwamitin ayyuka na majalisar

- Majalisar na neman cikakken bayani a kan jinkiri aikin jaran hanyan Bodo zuwa Bonny

- A shekarar bara ne gwamnan jihar Ribas ya nemi adin gwiwar kwamfanin NLNG don kammala aikin jaran hanyan cikin lokaci

Majalisar dattijai a ranar Laraba, 7 ga wata Yuni ta bukaci ministan makamashi, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ya gurfana a gaban ta a kan jinkiri aikin jaran hanyan Bodo zuwa Bonny da ke jihar Ribas.

Majalisar ta bukaci ministan ya gurfana a gaban ta don ba kwamiti kan ayyuka cikakken bayani a kan rashin gwamnatin tarayya da ta hada gwiwa da hukumar NLNG don kammala aikin jaran hanyan.

KU KARANTA: Kaico; Ashe Sanusi bai yi karya ba: An nemi Dala Miliyan 36.9 an rasa a Najeriya

A shekara ta 2016 ne gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya kusata kwamfanin NLNG da kuma kira ga kamfani da ta hada hannu da gwamnatin tarayya don zartar da aikin.

Toh fa: Majalisar Dattijan Najeriya ta bukaci wani babban ministan Buhari ya gurfana a gaban ta kan wani gwangila

Majalisar Najeriya

Aikin jaran babban titin Bodo zuwa Bonny mai kilometer 37 da ke jihar Ribas ita ce ta hada al'umman yankin Bodo a karamar hukumar Gokana da kuma Grand Bonny a karamar hukumar Bonny.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon da ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce yana kan hanya yana aiki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel