Rashin adalci: An wanke Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo kal

Rashin adalci: An wanke Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo kal

– Tsohon Darektan DSS na kasa yace sharri ake yi wa Osinbajo

– Wasu ‘Yan Arewa sun zargi Osinbajo cewa Yarbawa kurum da Kiristoci ya sani

– Gadzama yace Osinbajo mutum ne mai adalci da kuma kaunar kowa

Afakirya Gadzama ya kare Osinbajo daga korafin masu korafi

Tsohon Darektan Hukumar DSS din yace Osinbajo bai da nuna bambanci

Ana korafin cewa Osinbajo na nuna son kai wurin nadin mukamai

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo

Osinbajo mutum ne mai adalci-Tsohon Shugaban DSS

Afakirya A Gadzama Tsohon Darektan Hukumar DSS na Najeriya ya kira Jama’a su yi watsi da maganar cewa Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo mutum ne mai nuna bambanci da nuna son kai.

KU KARANTA: ka ga abin da Osinbajo yayi a Jihar Borno

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo

Osinbajo mutum ne mai adalci da kuma kaunar kowa

Gadzama yake cewa wasu ne kawai su ka kirkiri wannan magana domin su shafawa Mukaddashin Shugaban kasar bakin jini duk da irin biyayyar da yake yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa sam bai da fifita wasu Kabilar ko Yankin.

An zargi Osinbajo da dora mutanen sa; Yarbawa ne da Fastoci kadai tun da ya karbi mulki. Fadar Shugaban kasa tayi watsi da wannan magana inda tace rashin adalci ne ma a fadi hakan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko ana rashin Buhari a Najeriya kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel