Zamu ba Inyamurai da sauran baki cikakken tsaro a Katsina - Masari

Zamu ba Inyamurai da sauran baki cikakken tsaro a Katsina - Masari

Gwamnan jihar Katsina Rgh. Hon Aminu Bello Masari ya lashi takobin bayar da kyakkyawan tsaro ga 'yan kabilar Igbo mazauna Katsina, dama duk sauran bakin kabilun dake cikin jihar.

Gwamnan ya fitar da sanarwar hakan ne a ta bakin mai taimaka masa ta fannin yada labarai Abdu Labaran, inda ya bayyana cewa kabilar Igbon da ta yi fatsali da gargadin barin Arewa da kungiyar wasu matasan Arewa suka yana ta cewa su koma yankunan su, gwamnatin ya ce gwamnati ta shirya tsab domin bayar da kyakkyawan tsaro ga kowa ba tare da nuna bambancin kabilanci ko addini ko banbancin kasa ba.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya kuma kara da bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta zuba ido ta kyale duk wani wanda zai kawo barzanar cin mutinci ko kuntatawa wata kabila ko addini ko nuna wariyar kasa.

Zamu ba Inyamurai da sauran baki cikakken tsaro a Katsina - Masari

Zamu ba Inyamurai da sauran baki cikakken tsaro a Katsina - Masari

"Katsina gidan aminci ce, inda kowa da kowa keda ikon zuwa ya zauna ba tare da wata tsangwama ko tsoron cin mutuncin a ta kowane bangare ba.

"Ina kira ga duk baki mazauna Katsina musamman ma kabilar Igbo kar wani abu ya ba su tsoro,wannan gwamnatin ta shirya tsab wajen kare mutuncin duk wata bakila dake cikin jihar ba tare da nuna bambancin kabilanci ko addini da bambancin kasa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel