Lafiya jari: Abubuwa 7 da cin kwai yake samarwa a jikin dan adam

Lafiya jari: Abubuwa 7 da cin kwai yake samarwa a jikin dan adam

Ba yara kwai a lokacin da suke tasowa na da matukar amfani domin yana inganta girman jikin yaran saboda sinadarorin da kwan ke dauke da shi.

NAIJ.com ta samu labarin cewa bayanai na kwararru ya nuna cewa kwai na dauke da sinadarorin Vitamin A, B12, D, B6 wanda ke taimakawa wajen kara karfin garkuwan jiki yara musamman ‘yan kasa da shekaru 5.

1. Dafaffen kwai na bude kwakwalwan yaro.

2. Dafaffen kwai na dauke da sinadarin ‘lutein’ and ‘zeaxanthin’ wanda ke kara lafiyar idanuwar yaro.

3. Dafaffen kwai na kara karfin kashi a jikin yara kanana domin yana dauke da sinadarin Vitamin D.

Lafiya jari: Abubuwa 7 da cin kwai yake samarwa a jikin dan adam

Lafiya jari: Abubuwa 7 da cin kwai yake samarwa a jikin dan adam

4. Dafaffen kwai na dauke da sinadarorin leucine, phenylalanine, histidine, isoleucine, lycine, methionine, threonine, tryptophan da valine wanda suke taimakawa wajen gina jikin yaro da kuma kara masa jini.

5. Dafaffen kwai na kara girman kunba da gashin kan yara.

6. Omega-3 da ke cikin dafaffen kwai na taimakawa wajen bude kwakwalwar yaro kuma zai yi sauran gane abubuwa.

7. Dafaffen kwai na dauke da sinadarin Iron da ke taimakawa wajen samar da issashen jini a jikin yaro Wanda rashin shi yakan sa aga yaro na kumbura.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel