Aisha Buhari da wasu matan jiga-jigai sun yi wa Buhari da Najeriya addu'a (Hotuna)

Aisha Buhari da wasu matan jiga-jigai sun yi wa Buhari da Najeriya addu'a (Hotuna)

- Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari tare da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo sun yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa kasar addu’o’in hadin kai da zaman lafiya.

- Sun yi kiran ne a wani taron addu’o’i na musulmai da mabiya addinin kirista da aka gudanar a lokacin bude baki a jiya Alhamis a babban dakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja.

Yyain da ya ke gabatar da jawabin sa, Osinbanjo ya bayyana cewa Allah ne ya hada ‘yan Nijeriya a kasa daya domin su gina irin kasar da duniya za ta yi alfahari da ita.

Ya ce ‘yan Nijeriya a koda yaushe su sanya a ran su cewa Allah zai iya amfani da kasa Nijeriya wajen inganta rayuwar mutane da yawa.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya kara da cewa duk wadanda suke yada kiyayya a tsakanin jama’a su na yi ne kawai saboda son ransu, ba saboda ci gaban kasa ba.

Aisha Buhari da wasu matan jiga-jigai sun yi wa Buhari da Najeriya addu'a (Hotuna)

Aisha Buhari da wasu matan jiga-jigai sun yi wa Buhari da Najeriya addu'a (Hotuna)

A karshe ya yi godiya ga uwargidan Shugaban kasa da ta shirya taron shan ruwan da ya kunshi musulmai da kirista.

A na ta bangaren, Aisha Buhari, wacce ministan harkokin cikin gida Gen. Abdulrahman Dambazau (rtd.) ya wakilta a wajen taron ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su jimiri yi wa kasar addu’a, ta kuma gode masu da ci gaba da yi wa maigidan ta addu’o’in samun lafiya da suke yi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel