An bayyana musabbabin rashin jituwa tsakanin Buhari da Majalisa

An bayyana musabbabin rashin jituwa tsakanin Buhari da Majalisa

- Sanata Abba Aji ya bayyana dangantaka tsakanin Buhari da majalisa bata lalace ba

- Abba Aji yace majalisa ta cancanci yabo

Tsohon mashawarcin marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua Sanata Abba Aji ya bayyana dangantakar dake tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsagin majalisa batayi lalacewar da jama’a ke kambama tab a.

Abba Aji yace: “Gaskiya dantakar bata wani lalace ba, sanin kowa ne majalisa ce tushen siyasar Najeriya, ko a zamanin mulkin Soja majalisa kadai ake wargazawa saboda itace siyasa. Don haka dole ne su dinga sa idanu akan al’amuran bangaren zartarwa.

KU KARANTA: Bazawara ta kashe aurenta, ta biya mijinta sadakinsa, N80,000

“Sakamakon haka kuma, sai a dinga samun bambamcin ra’ayi tsakanin bangarorin biyu. Amma Saraki da Dogara sun san makaman aiki, ai kaga sun warare yan matsalolin da aka samu da siyasa.”

An bayyana musabbabin rashin jituwa tsakanin Buhari da Majalisa

Sanata Abba Aji

Dayake bayani akan dalilin rikici tsakanin majalisa da shugaba Buhari kuwa, Aji yace “Wannan shine karo na farko da jam’iyyar adawa ta hawo mulki, kuma APC bata sa ido akan alakar majalisa da bangaren zartarwa ba. Wannan shine karo na farko da majalisa ta zabi shuwagabanninta, a baya kuwa ba haka PDP take yi ba."

Daga karshe, Sanata Aji yace majalisa tana mutunta Buhari, don haka ta cancanci yabo, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayinku game da majalisa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel