Yankin Arewa: Matasan arewacin Najeriya sun lashe amai

Yankin Arewa: Matasan arewacin Najeriya sun lashe amai

- Yanzu dai kungiyoyin matasan arewa sun janye batun korar 'yan kabilar Inyamurai daga arewacin kasar

- Martani game da janye matakin kungiyoyin matasan arewacin Najeriya bisa neman kora ga 'yan kabilar Inyamurai daga yankin

- Jami'an tsaro ta yi barazanan kama kungiyoyin matasan arewa gami da batun cewa za su kori Inyamurai daga jihohin arewa

Kura ta fara lafawa a Najeriya bayan janye batun korar 'yan kabilar Igbo da matasan arewacin kasar suka kudiri aniya domin samun zaman lafiya. Lamarin da ya janyo martani da kungiyoyin masu fafatukar zaman lafiya da kungiyoyin matasan arewa ta tsakiya, a kan bukatar gwamnati ta gaggauta kiran taron kasa da sarakunan Najeriya da malaman addinai.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, duk da gargadin hukumomi da barazana daga jami'an tsaro kan kama kungiyoyin matasan arewa gami da batun cewa za su kori Inyamurai daga jihohin arewa. Kungiyoyin matasan sun kammala wani taro tattaunawa gami da tafka mahawara na tsawon kwanaki 2, inda kungiyoyin suka sake fitar wata takarda ta janye batun wa'adin da suka bai wa 'yan kabilar Inyamurai a arewacin kasa, domin kwantar da hankalin jama'a a Najeriya.

KU KARANTA: Zan sadaukar da jini na don tabbatar da zaman lafiya – Sarkin Katsina ga kabilar Igbo

Tuni dai shugabannin kungiyoyin da ke fafatukar kawo zaman lafiya suka fara tofa albarkacin bakinsu. Har dattawa daga yankin arewacin kasar suma dai sun gamsu da janye matakin matasan kan wannan lamari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel