Na zaci ba zaka iya zuwa Maiduguri ba - Gwamnan Borno ya cewa Osinbajo

Na zaci ba zaka iya zuwa Maiduguri ba - Gwamnan Borno ya cewa Osinbajo

- Tun bayan hawansu mulki, shekaru biyu, Yemi Osinbajo ne kawai yaje Borno

- Shugaba Buhari bai kai ziyara jihar Borno ko Sambisa ba

- Yemi Osinbajo ya duba 'yan gudun hijira a Borno

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya yaba da ziyara tare da jarumtar mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a jihar sa.

Mukaddashin shugaban kasa dai ya kai ziyarar aiki karo na biyu tun bayan hawansu karagar mulki a 2015, shekaru biyu kenan da suka gabata, inda ya duba ayyuka da kuma sansanonin masu gudun hijira da jihadin Boko Haram ya tagayyar a gabashin arewar Najeriya.

A duk shekarun nan biyu dai, shugaba Buhari wanda tsohon soja ne kuma jarumin janar, bai sami damar kai ziyara jihar Borno ba, duk da yaje kasashe da dama ziyarce-ziyarce.

'Na zaci ba zaka iya zuwa Maiduguri ba' Gwamnan Borno ya cewa Osinbajo

'Na zaci ba zaka iya zuwa Maiduguri ba' Gwamnan Borno ya cewa Osinbajo

Gwamnan jihar ta Borno ya ce: "A gaskiyar lamari, na zaci harin da Boko Haram suka kai a makon nan a birnin Maiduguri yasa na jefa shakkun ko baza ka iya zuwa ba, domin mun saba jin haka daga Abuja a (tsohuwar gwamnatin shugaba Jonathan)'", cewar gwamnan.

Ya kara da cewa: "A waccan gwamnati a 2014, mun shirya tsaf, muna jiran ziyarar shugaban kasa zuwa Chibok, kwatsam sai sako yazo mana cewa wai ya fasa zuwa.

"A washegarin sace 'yan matan Chibok matata da kanta ta tuka mota taje Chibok, washegari nima naje, amma wai shugaban kasa guda ya kasa zuwa ziyara wani yanki na kasarsa, wannan abin takaici ne matuka'.

"A gaskiya mun yaba da iya shugabancinka, da juriyarka, da mazantakarka da wannan ziyara".

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel