Gwamnatin jihar Legas tayi wa fursunoni 18 afuwa

Gwamnatin jihar Legas tayi wa fursunoni 18 afuwa

A ranan Alhamis ne majalisar afuwar jihar Legas ta baiwa hukumar kurkukun tarayya ta saki yan gidan yari 18 wadanda aka yankewa hukuncin rai da rai a gidan yarin Kirikiri.

Firsunonin wanda suka kunshi maza 15 da mata 3 suna daure ne rai da rai akan laifuffuka daban-daban kuma sun kwashe akalla shekaru 30 a kurkukun sun samu yanci.

An sake su ne bayan wasu tsattsaurun sharruda da aka basu na cigaba da rayuwa.

Yayinda ake bikin sakinsu a dakin taron kurkukun Kirikiri, shugaban majalisar, Prof. Oyelowo Oyewo,ya yabawa halin kirkin gwamnan jihar, Akinwumi Ambode na amfani da kujeransa wajen sakin firsinonin.

Bayan shekaru 30 a kurkukun Kirikiri, gwamnatin jihar Legas tayi wa fursunoni 18 afuwa

Bayan shekaru 30 a kurkukun Kirikiri, gwamnatin jihar Legas tayi wa fursunoni 18 afuwa

Kana kwamishanan shari’ar jihar, Mr Adeniji Kazeem, yayi kira ga firsunonin da ke cikin kurkuku har yanzu su kasance masu halaye na kwarai la’alla su samu irin wannan dama.

KU KARANTA: Osinbajo yayi buda baki da Musulmai a Aso Rock

Firsunonin sunyi matukar farin ciki tare da mika godaiyarsu ga gwamnan jihar na basu wata sabuwar daman na rayuwa da jama’a.

Sunyi alkawarin cewa zasu kasance masu halaye na kwarai kuma zasu kasance masu bin dokar kasa.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel