'Ka kakkabe ministocin Gwamnatinka' Limamin coci ya shawarci Buhari

'Ka kakkabe ministocin Gwamnatinka' Limamin coci ya shawarci Buhari

- Wani Bihop ya bukaci a sauya ministocin gwamnatin Buhari

- Yace a daina ture nauyi daga kan wadanda ya dogara a kafadunsu

- Ya ce in dai ana son ganin asalin chanji, to a chanja ministoci

Bishap Steven Kayode Akobe, na mujami'ar Anglica da ke Kabba a Kogi state, yayi kira ga shugaba Buhari da ya farka yasan lokaci yayi na sauke ministocinsa, domin saurin kawo sauyin wahalhalun da talakawa ke ciki na tattalin arziki.

Babban fasto din na magana ne yayin babban taro na cocin Anglica da ake yi a jihar ta Kogi, yace matsanancin wahalar da tattalin arziki ya jefa talakka ya haifar wa da jama'a yunwa.

Ya kuma bukaci shugaba Buhari ya maza ya sake sabon zubi a majalisar ministocinsa.

'Ka kakkabe Gwamnatinka' Limamin coci ya shawarci Buhari

'Ka kakkabe Gwamnatinka' Limamin coci ya shawarci Buhari

A cewar sa: "Lokaci yayi da za'a gani a kasa, domin wannan matsin tattalin arzikin ya kawo wahalhalun yunwa da talauci'

"Dole shugaba Buhari ya sauke wadannan tarin ministoci ya nada sabbi masu jini a jika, don wadannan tsofaffin su gaji, kuma ma yanzu dai ya kamata Buhari ya duba mai zayyi wa mutanen Najeriya, ba wai mai mutanen Najeriya zasuyi masa ba."

Ana dai taragon karshe a wa'adin shekaru hudu a mulkin APC da shugaba Buhari, kuma har yanzu Ministocin da ya nada sune suke kan karagar mulki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel