Bazawara ta kashe aurenta, ta biya mijinta sadakinsa, N80,000

Bazawara ta kashe aurenta, ta biya mijinta sadakinsa, N80,000

- Wata mata ta nemi kotu ta kashe aurenta da mijinta

- Kotu ta raba auren, matar ta biya mijin N80,000

Wata kotun jihar Filato dake zama a garin Jos ta raba auren wasu ma’aurata Rukayya Ahmed da Alkasim Ahmed, biyo bayan bukatar hakan da matar tayi ma kotu.

Ita dai Rukayya, yar bautan kasa ce, kuma mazauniyar garin Jos ce, ta nemi kotu data kawo karshen zamanta da mijinta Alkassim, sakamakon ta daina son sa ko kadan, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito.

KU KARANTA: Ban ga dalilin da zai sa na ajiye Azumi saboda harkar ƙwallo ba – Inji Ahmed Musa

Rukayya ta shaida ma kotu cewar bukatar tata tayi daidai a musulunce, tun da dai ita bata son sa, kuma bata bukatar cigaba da zama da shi, inji rahoton majiyar NAIJ.com.

Bazawara ta kashe aurenta, ta biya mijinta sadakinsa, N80,000

Kotun Jos

Da aka karanta ma mijin Rukayya batun da kuma bukatar da matarsa ta kawo ma kotu, sai bai musanta batun ba, haka ta sanya a ranar Alhamis 8 ga watan Yuni, Alkali mai shari’a Yahaya Ahmed ya tabbatar da kashe auren.

Cikin hukuncin da alkali ya yanke, ya bukaci Rukayya ta biya Alkasim kudi, wuri na gugan wuri har N80,000, sadakin da ya biya na aurenta da fari, kamar yadda shari’a ta tanada.

Abinka da mai nema, nan da nan ba tare da bata lokaci ba, Rukayya ta biya tsohon mijin nata N80,000 lakadan, tabbacin aure ya mutu kenan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaki iya rantsuwar aure?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel