Kungiyar dattawan Arewa sun goyi bayan matasan Arewa

Kungiyar dattawan Arewa sun goyi bayan matasan Arewa

- Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya ce matasan Arewa sun yi barazanar korar yan kabilar Igbo ne domin maida martani ga hallayar su

- Ango Abdullahi ya bayyana cewa matasan Arewa na nuna fushin su ne kan rashin da’a na matasan Igbo da dattawan su

- Dattawan na Arewa sun ce ya zama dole shugabannin Igbo da matasansu su ajiye girman kai da kuma dakatar da mummunan dabi’un su

Kakkain kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya goyi bayan matasan arewa na cewa Igbo su bar yankin Arewa cikin watanni uku.

Ango Abdullahi, tsohon shugaban makarantar jam’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria ya fada ma jaridar Guardian a kan waya cewa umurnin da matasan arewa suka bayar ya kasance martani ga mummunan dabi’un bakinsu.

KU KARANTA KUMA: Sufeton ‘Yan sanda ya yi umarni da a kama shugabannin matasan Arewa

Kungiyar dattawan Arewa sun goyi bayan matasan Arewa

Kungiyar dattawan Arewa sun goyi bayan matasan Arewa

Ya ce matsan arewa na nuna fushin su da gajiyar su a kan abun da suka bayyana a matsayin mumunan dabi’un matasan kabilar Igbo da dattawan su.

Dattawan na Arewa sun ce ya zama dole shugabannin Igbo da matasansu su ajiye girman kai da kuma dakatar da mummunan dabi’un su.

A halin da ake ciki Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris Kpotun ya bada umarnin kama shugabannin kungiyoyin Arewan da suka yi wa ‘yan kabilar Igbo barazana ta hanyar basu wa’adin watanni uku su bar yankin Arewa.

Ya bada wannan umarni ne a jiya Alhamis, 8 ga watan Yuni a lokacin da ya ke zantawa da kwamishinonin ‘yan sanda na kasa baki daya a babban birnin tarayya Abuja.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel