Zan sadaukar da jini na don tabbatar da zaman lafiya – Sarkin Katsina ga kabilar Igbo

Zan sadaukar da jini na don tabbatar da zaman lafiya – Sarkin Katsina ga kabilar Igbo

- Sarkin Katsina, ya ce Najeriya zata ci gaba da kasance tsintsiya madaurin ki daya duk da yawan kabilun ta

- Ya ce a shirye ya ke ya sadaukar da jinin sa domin wanzar da zaman lafiya

- Sarkin ya bukaci kabilu daban-daban dake zaune a jihar da su kwantar da hankulansu kamar yadda masarautar da kuma gwamnatin jihar zata dauki duk mataki da ya kamata

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, ya bayyana cewa Najeriya zata ci gaba da kasance tsintsiya madaurin ki daya duk da yawan kabilun ta.

Kabir ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a fadar sa dake Katsina, lokacin da ya ke jawabi ga shugabannin kabilar Igbo da sauran yan Najeriya mazauna jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Kimanin mutane 20 akayi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna

“Ina sharhi ne a kan barazanar kora da wasu kungiyar mutane da suka kasance makiyan zaman lafiya suka yi ma wasu ‘yan Najeriya dake zaune a Arewa.

“A nan Katsina, na shirya sadaukar da jini na don tabbatar da zaman lafiya da kuma kare dukkan ‘yan Najeriya dake zaune a jihar,” cewar sa.

Sarkin ya bukaci kabilu daban-daban dake zaune a jihar da su kwantar da hankulansu kamar yadda masarautar da kuma gwamnatin jihar zata dauki duk mataki da ya kamata domin tabbatar da warzuwan zaman lafiya.

Sarkin ya bukace su da su ci gaba da addu’a don samun zaman lafiya da hadin kai a kasar, domin tabbatar da ci gaba mai dorewa, kamfanin dillancin labarai na Najeriya ta ruwaito.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel