Tuni ma 'Yan kabilar Ibo sun fara tserewa daga arewa.

Tuni ma 'Yan kabilar Ibo sun fara tserewa daga arewa.

- Akwai miliyoyin 'yan kabilar Ibo a ko ina a garuruwan arewa

- Ana yawan tsangwamar kabilar Ibo a arewa

- A baya ma da irin haka ta kai kasar najeriya ga yakin basasa

Mai kai wa jaridar daily post rahoto daga Kaduna, ya garzaya tashar motoci a Kaduna a jiya alhamis, inda a cewarsa, ya gane wa idonsa yadda jama'ar kabilar Ibo da yawa na ficewa daga yankin na arewa, suna komawa gida.

Godwin Ameh, yace wannan ya biyo bayan wa'adi da wasu samarin da ke kiran kansu samarin arewa suka yi na cewa dole kafin watanni ukku su fice musu daga yankinsu, tunda wai a cewarsu, basu gode da zaman cin arzikin da suke ba.

'Tuni ma 'Yan kabilar Ibo sun fara tserewa daga arewa.'

'Tuni ma 'Yan kabilar Ibo sun fara tserewa daga arewa.'

A taunawa da yayi da wani mai niyyar hijiras, Ifeanyi Odozie, wanda ke sayar da kayan wuta, yace: "Ni bazan yi ganganci da rayuwar iyali na ba, shekaru na talatin a nan amma dole in koma kauye, zaman ya isa haka, zan dawo bayan na kaisu gida, in zo in sayar da dukiyoyi na".

Da aka tuna masa ai gwamnati ta shawo kan lamarin sai ya kada baki yace: "Sanda za'a far mana gwamnatin tana wurin ne? kaga an kama masu irin wadannan kashe kashe a baya ne? Banson ganganci da rayuwa ta, zanje kauye in huta, in naga jijiyoyin wuya sun kwanta na iya dawowa.

Anga wata mata ma da tukwane da katifu na irin wannan batu. Mai rahoton yace a Kano ma yaga irin wannan hijira a tashoshin mota.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel