Bayyana mana inda kudinmu yake cikin sati uku ko muje Kotu - Lauyan Najeriya ga Buhari

Bayyana mana inda kudinmu yake cikin sati uku ko muje Kotu - Lauyan Najeriya ga Buhari

- Wani lauyan me kare hakkin dan Adam ya ce gwamnatin nan ta karo talauci ne

- Ya baiwa Buhari sati uku ko ya fito da kudin da aka kamo ko suje kotu

- Ya kuma nemi sanin inda kudaden su ke

A kokarinsa na ganin anyi adalci kuma an rage wa talakka zafin talauci, wani lauya kuma dan rajin kare hakkin jama'a, Mike Ozokheme SAN, ya rattaba wasika ga shugaba Buhari, ta hannun mukaddashin sa Yemi Osinbajo, cewa lallai su fito ma da 'yan Najeriya kudinsu ko ya kai su kotu.

A dai wasikar, ya jra wa gwamnatin tarayya wasu tambayoyi kamar haka: "Shin ina duk kudaden suke ajje ma ne? Ku ma kun boye su a makabarta ne ko a gida? ko kuwa kun kai su babban banki na CBN?"

Ya ce ajje kudin a boye bai kara ma talakka komai ba, kuma ma wannan gwamnatin ta kara wa jama'a talauci. 'A fito da su don mu mora'.

'Bayyana mana inda kudinmu yake cikin sati uku ko muje Kotu, shugaba Buhari'

'Bayyana mana inda kudinmu yake cikin sati uku ko muje Kotu, shugaba Buhari'

Ya ce: "A Kullum sai dai muji an kama kudi a can, an kamo a nan, amma tsit ba wani taimako, ba kuma bayanai a kan yadda aka yi da su.

'To ko cikin uku ka fito kayi mana bayanin yadda abun yake, ko kuwa kaji ka a kotu."

A baya dai, an fi zargin wasu lauyoyin da zuwa su daure kudaden a kotu, domin barayin su dawo su gaje kudin, Ministan ilmi a sau da dama yakan yi bayanin cewa in ba an gama warware matsalar a kotuna ba, baza a iya taba kudaden ba, wadanda sun kai tiriliyan na nairoro kusan ukku.

Wa'adin gwamnatin nan dai ya kusa karewa, kuma kuraye da yawa suna neman damar dawo wa karagar mulki, ganin dumbin kudin da gwamnati ta tara.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel