Ban ga dalilin da zai sa na ajiye Azumi saboda harkar ƙwallo ba – Inji Ahmed Musa

Ban ga dalilin da zai sa na ajiye Azumi saboda harkar ƙwallo ba – Inji Ahmed Musa

- Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa yace zai yi Azumi

- Ahmed Musa yace shida abokansa ba zasu fasa Azumi ba

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa ya dage kai da fata cewa lallai da shi da abokansa musulmai dake kungiyar ba zasu fasa Azumtar Ramadan ba saboda kwallo.

Ahmed Musa dai na daga cikin yan wasan da zasu fafata da kasar Afirka ta kudu a ranar Asabar a garin Uyo, sai dai dan wasan yace bai ga dalilin da zai say a ajiye azumi ba saboda wasan ba.

KU KARANTA: Siriki ya danƙara ma sirikarsa ciki, ya sallami matarsa

A yayin gabatar da taron manema labaru a garin Uyo, Musa yace ko a gasar cin kofin Duniya da aka yi a kasar Brazil, sai da yayi azumi, inda ya kara da cewa shi fa wannan ba wani abu bane, kamar yadda Premium Times ta ruwaito

Ban ga dalilin da zai sa na ajiye Azumi saboda harkar ƙwallo ba – Inji Ahmed Musa

Ahmed Musa

“Azumin Ramadan akwai wahala, amma mun saba, ba wani sabon abu bane a wajen na, ba zamu daina Azumi ba saboda kwallo.” Inji Musa

Musa ya cigaba da fadin “Na buga wasa a Brazil a shekarar 2014 ina Azumi, kuma gaba daya wasan na buga, amma dai mai horar da mu ne zai tantance wadanda zasu buga, idan ya samu zamu buga wasa.”

Ban ga dalilin da zai sa na ajiye Azumi saboda harkar ƙwallo ba – Inji Ahmed Musa

Super Eagles yayin Atisaye

Sauran yan wasa Musulmai dake kungiyar Super Eagles sun hada da Moroof Youssef, Shehu Abdullahi, da Alhassan Ibrahim ‘Muazzam’.

Ko a wasan da Najeriya ta buga a satin data gaba da kasar Togo, sai da Ahmed Musa ya nuna gwanintansa inda ya zura kwallaye biyu a ragar Togo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Auren mutu ka raba?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel