Dubun wani ɓarawon babur da mota ta cika a Kano (Hoto)

Dubun wani ɓarawon babur da mota ta cika a Kano (Hoto)

- Asirin wani ƙasurgumin ɓarawon babura da motoci a Kano ya tonu

- Abubakar Auwalu ya shiga komar yansanda ne a unguwar Hotoro

Wani fitinannen barawo daya addabi mazauna yankin Hotoro na jihar Kano, Abubakar Auwalu ya shiga komar yansanda, inji rahoton Daily Trust.

Da yake bayyana ma manema labaru gawurtaccen barawon, Kaakain rundunar Yansandan jihar, DSP Magaji Musa Majia yace barawon yak ware wajen yin cinikin karya na siyan motoci da babura, amma da zarar ya dauka zai yi gwaji, sai ya tsere da babur din mutane.

KU KARANTA: Shekara 19 da rasuwa: Janar Abacha, ‘sai bayan baka ake’

“Mun kama Auwalu ne a ranar 24 ga watan Mayu a lokacin da ya fada komar mu, mun kama shi da wata motar sata kirar Golf 3, da kuma babur Lifan guda 2” inji Majia.

Dubun wani ɓarawon babur da mota ta cika a Kano (Hoto)

Auwalu

Daga karshe Majia ya shaida ma majiyar NAIJ.com cewa nan bada dadewa ba zasu kammala bincikensa tare da gano sauran kayayyakin daya sata a waurare daban daban cikin jihar Kano.

Ya za'ayi idan matarka tafi ka samun kudi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel