Sufeton ‘Yan sanda ya yi umarni da a kama shugabannin matasan Arewa

Sufeton ‘Yan sanda ya yi umarni da a kama shugabannin matasan Arewa

- Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya ya bada umarnin kama shugabannin kungiyoyin Arewan da suka yi wa ‘yan kabilar Igbo barazana

- Ya ce babu wani mutum da ya isa ya hana wani zama ko neman abincinsa a kowane yanki cikin fadin kasar nan

- Ya umurci rundunar da su kasance cikin shiri don ganin matasan ba su aiwatar da nufin su ba

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris Kpotun ya bada umarnin kama shugabannin kungiyoyin Arewan da suka yi wa ‘yan kabilar Igbo barazana ta hanyar basu wa’adin watanni uku su bar yankin Arewa.

Ya bada wannan umarni ne a jiya Alhamis, 8 ga watan Yuni a lokacin da ya ke zantawa da kwamishinonin ‘yan sanda na kasa baki daya a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA KUMA: KALLI dan wasan Saudiyya daya tilo da ya halarci taron wadanda harin Landan ya cika da su

“A matsayinku na kwamishinonin ‘yan sanda, da mataimakan sufeto janar na ‘yan sanda da ke shugabantar rundunonin ‘yan sanda na shiyya-shiyya hakkinku ne ku tabbatar da cewa wadannan mutane ba su aiwatar da wannan ikirari nasu ba.

“Ina so mu kasance cikin shirin ko ta kwana don ganin cewa wadancan mutane basu aiwatar da manufarsu ba.

“Babu wani mutum da ya isa ko yake da ikon hana wani zama ko neman abincinsa a kowane yanki cikin fadin kasar nan”, inji Sufeto Janar Ibrahim Idris Kpotun.

Shin kundauki rundunar yan sandan Najeriya a matsayin abokai?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel