Jami’an Ýansanda sun lallasa wani direban ‘A-daidai-ta’

Jami’an Ýansanda sun lallasa wani direban ‘A-daidai-ta’

- Wasu jami’an Yansanda a jihar Legas sun lakada ma direban yar kurkura duka

- Direban Napep din ya ajiye fasinja ne a daidai kofar shiga kamfanin

Wasu jami’an Yansanda dake tsaron wata kamfani a jihar Legas sun lakada ma direban yar kurkura da aka fi sani da suna Keke-Napep dukan tsiya a sanadiyyar musu da ja-in-ja da yayi dasu.

Yansandan suna tsaron kamfanin ‘EISNL Engineering Solutions and Drive Ltd’ ne dake lamba 9 titin Adeniyi Jones, unguwar Ikeja, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Yayi shigar mata don ya zana ma budurwarsa jarabawa

Shaidun gani da ido sun shaida ma majiyar NAIJ.com cewar direban Napep din mai suna Michael Akande ya ajiye fasinja kenan a daidai kofar shiga kamfanin, sai Yansandan suka fara tuhumarsa akan dalilin da yasa ya tsaya da Napep din a gaban kamfanin.

Jami’an Ýansanda sun lallasa wani direban ‘A-daidai-ta’

Direban ‘A-daidai-ta’

Daga nan ne fa sai musu da kace nace ta shiga tsakanin yansandan da direban, ba tare da bata lokaci ba yansandan suka diro daga motocinsu suka fara horar da direba Michael.

Shima wani shaidan gani da ido yace, “Ina kokarin tsayawa da mota ta inyi siyayya ne lokacin da lura da direban da yansandan suna cacar baki, yansandan sun zo da wasu turawa ne, kuma sun bukaci direban ya dauke Napep dinsa daga kofar shiga kamfanin, amma yaki ji. Daga nan ne suka fara jibgarsa, har sai daya fadi sumamme, inda ya kwashi awanni biyu a kasa.”

Bayan farfadowarsa, direban ya bayyana nasa labarin: “Na ajiye wani daga cikin ma’aikatan kamfanin ne, ina kokarin bashi canjinsa kenan sai Yansandan suka diro, duk kokarin da nayi in matsar da Napep taki tashi, daga nan ne fa Yansandan suka far min da duka, har da kan bindiga, suka kaarya min kafa.”

Daga karshe sakamakon taruwar sauran direbobin Napep, sai ma’aikatan kamfanin suka garzaya da shi asibiti.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel