Kada wani dan Kabilar Igbo ya tsorata da barazanar da matasan Arewa su kayi masu – Gwamnonin Jihohin Igbo

Kada wani dan Kabilar Igbo ya tsorata da barazanar da matasan Arewa su kayi masu – Gwamnonin Jihohin Igbo

- Gwamnonin yankin Kudu Maso Gabas sun bukaci ‘yan kabilar Igbo dake Arewa da su yi burus da barazanar kungiyoyin matasan Arewa

- Sun kuma bukaci gwamnonin Arewa da sub a ‘yan kabilar su kariya a yankin su

- Har ila yau sun ce ya kamata a yi ma tufkar hanci don gudun maimaita tarihi

Gwamnonin yankin Kudu Maso Gabashin kasar Najeriya sun yi kira ga ‘yan kabilar Igbo dake zaune a yankin arewacin kasar da su yi watsi da barazanar da wasu kungiyoyin matasan Arewa su kayi na cewa sun basu watanni uku su tattara yanasu-yanasu su bar yankin su.

Shugaban kungiyar gwamnonin yankin kuma gwamnan jihar Abia, David Umahi ne ya sanar da hakan bayan sun kammala taron kungiyar gwamnonin yankin na kudu.

KU KARANTA KUMA: Yara biyu sun mutu yayinda bam ya tashi a Fadaman Rake dake AdamawaYara biyu sun mutu yayinda bam ya tashi a Fadaman Rake dake Adamawa

Kada wani dan Kabilar Igbo ya tsorata da barazanar da matasan Arewa su kayi masu inji Gwamnonin Jihohin Igbo

Gwamnonin Kudu sunce Kada wani dan Kabilar Igbo ya tsorata da barazanar da matasan Arewa su kayi masu

Har ila yau ya yi kira ga shugabannin Arewa da su tabbata sun ba ‘yan kabilar Igbo dukwani kariya da suke bukata a yankin su na Arewa.

Ya ce dole a dauki kwakwaran mataki akan irin wadannan matasa da kuma yi wa tufkar hanci don gudun kada a maimaita abinda ya faru a baya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com a kasa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel