Yara biyu sun mutu yayinda bam ya tashi a Fadaman Rake dake Adamawa

Yara biyu sun mutu yayinda bam ya tashi a Fadaman Rake dake Adamawa

- Wani tashin bam ya afku a yankin Fadaman Rake dake karamar hukumar Hong a jihar Adamawa

- Al'amarin ya faru ne daidai lokacin da ake shirin bude bakin azumin Ramadan

- Yara biyu ne suka mutu sanadiyar harin

Wani tashin bam ya afku a yankin Fadaman Rake dake karamar hukumar Hong a jihar Adamawa, a daren ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni, wanda ya yi sanadiyar mutuwar yara guda biyu.

Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 7 na yamma, yayinda mazauna yankin ke shirin bude bakin azumin.

Wannan ya sa mazauna yankin da dama sun gudu sun bar gidajensu.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo a Maiduguri : Ya kai ziyara ga wadanda harin Boko Haram ya shafa (Hotuna)

Wani dan agaji mai suna Baba Yerima ya bayyana yadda lamarin ya auku.

Ya ce wani mutum ne ya zo a cikin mota kirar Starlet ya kira yara guda biyu da ke wasa, ya baiwa daya daga cikin su bakar leda da cewar sako ne da zai kaiwa mahaifin shi.

Barin yaran daga gurin ke da wuya aka ji tashin bam din. Babu daya daga cikin su da ya yi rai, yayin da wasu mutane uku suka jikkata.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jahar Othman Abubakar ya tabbatar da faruwa al’amarin.

Ya ce tuni an garzaya da jikkatattun zuwa asibitin Hong.

NAIJ.com ta tattaro cewa wannan hari dai na zuwa ne kimanin awanni 24 bayan mayakan Boko Haram sun kai wasu hare hare a Maiduguri da ke jahar Borno wanda ya haddasa rasuwa akalla mutane 17.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Menene ra'ayinku game da dawowar shugaba Buhari nan ba da jimawa ba?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel