Katsina: Gwamnatin tarayya ta dukufa don kafa matatar man a Katsina

Katsina: Gwamnatin tarayya ta dukufa don kafa matatar man a Katsina

- Gwamnatin tarayya ta ce ta duƙufa wajen kafa matatar man fetur a yankin arewa maso yammacin kassar musamman jihar Katsina

- Wannan shirin zai kara adadin matatun man fetur a Najeriya da kuma gyara wadanda ake da su don kasar ta iya dogara da kanta

- Gwamnati na neman masu zuba jari da zasu sanya dukiyarsu ga aikin kafa matatar man

Gwamnatin tarayya ta ce ta duƙufa wajen kafa matatar man fetur a jihar Katsina, ta yadda ƙasar za ta samu ƙarfin tace man da ake buƙata har ma da na ƙasashe maƙwabta.

Matakin wani yunƙuri ne na kara adadin matatun man fetur a Najeriya da kuma gyara wadanda ake da su don kasar ta iya dogara da kanta.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Malam Umar Faruk babban jami'i mai kula da ayyuka na musamman ga ministan albarkatun man fetur na Najeriya ya ce ko da yake, Najeriya a yanzu ba tada kuɗin da za ta gyara illahirin matatun kasar, amma ta dukufa wajen nemo masu zuba jari da zasu sanya dukiyarsu a wannan aiki.

Gwamnatin tarayya ta dukufa don kafa matatar man a Katsina

Gwamnatin tarayya ta duƙufa wajen kafa matatar man fetur a jihar Katsina

Ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kuduri aniyar kafa matatar mai a duk shiyyoyin kasar 6, don tabbatar da wadatarsa.

Umar Faruk ya ce kafa matatar man fetur a Katsina zai ba wa Najeriya damar tallafawa wajen tace man da jamhuriyar Nijar take hakowa a ƙasarta.

Ya ce Najeriya na gudanar da tuntuɓa da masu sha'awar zuba jari don ganin yadda za a farfaɗo da matatun man kasar.

"Ba wai zasu zo da kuɗi ne a sayar musu da matatun ba, za su zo a haɗa gwiwa a yi wannan gyara ta yadda matatun za su kai matsayin da za su rika aiki (gadan-gadan).

KU KARANTA: Majalisar dattawa tayi amai ta lashe, ta soke takardan karin N5 kan farashin man fetur

Ya kuma ce kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarni na tabbatar da gyara ɗaukacin matatun mai na ƙasar, ministan man fetur Mista Ibe Kachukwu ya bullo da tsare- tsaren nemo masu zuba jarin da za a haɗa hannu da gwamnati.

A cewarsa hakan ba yana nufin gwamnati na da niyyar sayar da matatun mai na kasar ba.

A baya dai an ambato Ibe kachukwu na cewa rashin tsare-tsare da za a dade ana cin gajiyarsu ne ya kawo tabarbarewar al'amura a bangaren samar da man fetur na Nijeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon da ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce yana kan hanya yana aiki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel