Gwamnan Bauchi ya kammala gina cibiyoyin kiwon lafiya 19 da tituna (Hotuna)

Gwamnan Bauchi ya kammala gina cibiyoyin kiwon lafiya 19 da tituna (Hotuna)

- Gwamnatin jihar Bauchi ta kammala gina wasu gina cibiyoyin kiwon lafiya 19 da tituna a fadin jihar

- Mai magana da yawun gwamnan ya ce ginin asibitocin na hadin guiwa ne tsakanin gwamnatin jihar da shirin cimma muradun karni mai dorewa (SDGs)

- Za a zuba kayayyakin aiki na zamani a duka cibiyoyin kiwon lafiyar hade da motocin dibar mararsa lafiya

Hotunan wasu daga cikin asibitocin yara kenan da gwamnatin gwamna Barista M.A ya gina a fadin jihar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, mai magana da yawun gwamnan a fannin sadarwa, Shamsudeen Abubakar Lukman ya ce duka asibitoci 19 an kammala ginasu hadi da gidajen kwanan likitoci da kuma ban daki.

Ya ce aikin ginin asibitocin na hadin guiwa ne tsakanin gwamnatin jihar da shirin cimma muradun karni mai dorewa (SDGs).

Gwamnan Bauchi ya kammala gina cibiyoyin kiwon lafiya 19 da tituna (Hotuna)

Daya da cikin asibitin yara kenan da gwamnatin gwamna Barista M.A Abubakar ya gina

Mista Shamsudeen ya kuma kara da cewa za a zuba kayayyakin aiki na zamani a duka cibiyoyin kiwon lafiyar hade da motocin dibar mararsa lafiya.

Gwamnan Bauchi ya kammala gina cibiyoyin kiwon lafiya 19 da tituna (Hotuna)

Cibiyan kiwon lafiyan da gwamnan Bauchi ya gina

KU KARANTA: Maganganun wasu manyan mutane 5 game da shirin sallamar Inyamurai daga Arewa

A wani labari makamancin wannan kuma gwamnan ya kammala gina hanyar mahadar Fadaman Mada dake jihar.

Gwamnan Bauchi ya kammala gina cibiyoyin kiwon lafiya 19 da tituna (Hotuna)

Wani titi zuwa tagwayen hanya tare da fitulun gefen hanya

An fadada titunan zuwa tagwayen hanyoyi tare kuma da fitulun gefen hanya.

Gwamnan Bauchi ya kammala gina cibiyoyin kiwon lafiya 19 da tituna (Hotuna)

Daya daga titunan zuwa tagwayen hanya tare da fitulun gefen hanya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Femi Fani Kayode ya bayyana cikakken bayani da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel