Inyamurai: Ku zo mu ba ku mafaka Inji wasu ‘Yan Arewa

Inyamurai: Ku zo mu ba ku mafaka Inji wasu ‘Yan Arewa

– ‘Yan Yankin Arewa-maso-tsakiya sun ce a daina masu kallon Hausa-Fulani

– Mutanen Yankin su ka ce Arewa suna ta tara don kuwa ba a zama daya ba

– Shugaban Matasan Yankin ya bayyana wannan kwanan nan

Wata Kungiya a Arewa ta nemi Inyamurai su bar kasar

Sai dai ‘Yan Yankin tsakiyar Arewa sun ce su na maraba da Inyamurai

Emma Zompa yayi wannan jawabi bayan wannan abu ya faru

Inyamurai: Ku zo mu ba ku mafaka Inji wasu ‘Yan Arewa

Gwamnonin Arewa sun yi tir da shirin korar Ibo

Wasu matasan Arewa sun yi kira Inyamurai su bar kasar su nan da kwanaki 90 watau watanni uku. Sai dai ‘Yan Yankin Arewa maso tsakiya sun nesanta kan su daga wannan kira inda su ka ce za su karbi Inyamurai da hannu biyu.

KU KARANTA: Na kusa da Osinbajo na nema su hana Osinbajo mulki

A cewar Shugaban matasan Yankin Emma Zompa sun sha ban-ban da asalin mutanen Arewa wadanda mafi yawa su ke Hausa/Fulani. Zompa yace a daina yi masu kallon ‘Yan Arewa tu-kuf. Wani Tsohon Ministan Najeriya Femi Fani-Kayode ya ji dadin wannan kalamai.

Wata Kungiya ce ta samarin Arewa tayi kira da Inyamurai su bar Arewacin kasar. Sai dai dama ba su gamsu da hakan ba, kuma har Gwamnan Jihar Kaduna ya sa a kama masu wannan barazana.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani mai kama da Marigayi tsohon Kocin Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel