UCL: Ka ji abin da Gwamnan Ribas yayi bayan Real Madrid sun yi nasara

UCL: Ka ji abin da Gwamnan Ribas yayi bayan Real Madrid sun yi nasara

– Kungiyar Real Madrid ce ta lashe kofin Champions league na bana 2017

– Hakan ta sa Gwamna Nyesom Wike ya hada ‘yar liyafa

– Gwamna Wike da wasu ‘Yan PDP sun yi bikin murna

Real Madrid ta doke Juventus a wasan karshe na kofin Champions league

Gwamna Wike na Jihar Ribas yayi walima don murna

Gwamnan zai kuma bude makarantar koyon kwallon na Real Madrid

UCL: Ka ji abin da Gwamnan Ribas yayi bayan Real Madrid sun yi nasara

UCL: Ka ji abin da Gwamnan Ribas yayi bayan Real Madrid sun yi nasara

Babban Dan wasan Real Madrid watau Ronaldo ya zura kwallaye biyu a wasan su da Juventus a wasan karshe na makon. Juventus ta sha kashi ne a hannun Madrid da ci 4-1 a Birnin Cardiff wanda hakan ta sa Gwamna ya kira walima.

KU KARANTA: Za a binciki ayyukan Buhari a Neja-Delta

UCL: Ka ji abin da Gwamnan Ribas yayi bayan Real Madrid sun yi nasara

UCL: Gwamna Wike na Jihar Ribas yayi walima don murna

Gwamnan Jihar na Ribas ya hada walima domin Jama’a su taya sa murnar lashe wannan kofi. An ga Gwamnan tare da rigar Kungiyar Real Madrid da kuma wata kamar mai dakin sa suna ta faman murna bayan Kungiyar ta doke Juventus ta ajiye tarihi.

Ku na sane cewa Real Madrid ta kara lashe kofin Nahiyar Turai na UEFA Champions league a daren jiya inda ta lallasa. Dan wasa Ronaldo ne ya kara gamawa da kwallayen da su ka fi na kowa bayan ya jefa 2 a wasan karshe.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya za ayi idan mace ta fi mijin ta albashi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel