Maganganun wasu manyan mutane 5 game da shirin sallamar Inyamurai daga Arewa

Maganganun wasu manyan mutane 5 game da shirin sallamar Inyamurai daga Arewa

– Wata Kungiya a Arewa ta nemi Inyamurai su bar kasar

– Da dama dai na cewa ba da su ba

– Shugabannin Yankin sun musanya sanin wannan magana

Wasu matasan Arewa sun yi kira a bar kasar su

Da dama dai na sukar wannan umarni da aka kawo

Manyan kasar da sauran Jama’a na ta tofa albarkacin bakin su

Maganganun wasu manyan mutane 5 game da shirin sallamar Inyamurai daga Arewa

Korar Inyamurai: An maidawa Yankin Arewa martani

Wata Kungiya ta samarin Arewa tayi kira da Inyamurai su bar Yankin kasar cikin watanni 3 rak. Sai dai dama ba su gamsu da hakan ba, kuma har Gwamnan Jihar Kaduna ya sa a kama su. Ga yadda su ke fada.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun kama wani mutum dauke da sashen jikin mutum

1. Goodluck Jonathan

Tsohon Shugaba Jonathan yayi kira ta shafin yada labarai na Twitter cewa babu wanda ya isa ya hana Inyamurai zama a duk inda su ka so a fadin Najeriya.

Maganganun wasu manyan mutane 5 game da shirin sallamar Inyamurai daga Arewa

Korar Inyamurai daga Arewa: Ka da ku yarda Inji Jonathan

2. Femi Fani-Kayode

Tsohon Ministan sufurin jirgin sama cewa kuwa yake yi Matasan na Arewa su na wasa ne da Inyamuran kuma su bi a sannu.

3. Jam'iyyar APC

Wani babban Dan Jam’iyyar APC, Timi Frank ya kira manyan Arewan su gargadi matasan da ke kokarin tada wani rikici.

Maganganun wasu manyan mutane 5 game da shirin sallamar Inyamurai daga Arewa

Wata Kungiya ta nemi Inyamurai su bar Arewa

KU KARANTA: Fada tsakanin Gwamnati da sashen shari'a

4. Gwamnatin Tarayya

Ministan yada labarai da ma na harkokin cikin gida watau Alhaji Lai Mohammed da kuma Janar Abdurrahman Dambazzau yace za a hukunta wadanda aka kama.

5. Shugabannin Arewa

Gwamnoni da sauran manyan Arewa dai tuni su kace ba da su ba a cikin wannan magana na cewa za a kora Inyamurai daga Yankin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko 'Yan Najeriya sun yi kewar Shugaba Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel