Mutane 14 ne suka rasa rayukansu yayinda 24 suka jikkata a harin da Boko Haram ta kai Maiduguri

Mutane 14 ne suka rasa rayukansu yayinda 24 suka jikkata a harin da Boko Haram ta kai Maiduguri

- Rundunar 'yan sanda ta ce akalla mutane 14 ne suka mutu a harin da yan Boko Haram suka kai Borno

- Har ila yau mutane 24 ne suka jikkata a mummunan harin

- Ciki har da 'yan kunar bakin waken da suka kai harin

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce mutane 14 ne suka rasa rayukansu a harin bam da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Victor Osoku ya shedawa manema labarai cewa harin ya cika ne da yan fararen hula goma sha daya da kuma ‘yan kunar bakin wake uku, yayinda mutane 24 suka jikkata.

KU KARANTA KUMA: Ministan cikin gida, Dambazau ya tofa albarkacin bakinsa kan barazanar da akayiwa Igbo

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Borno Damian Chukwu ya shedawa wani taron manema labarai a birnin Maiduguri cewa, 'yan Boko Haram din sun yi amfani da bindigogin kakkabo jirgi yayin harin da aka kai ranar Laraba.

Har ila yau kakakin rundunar sojan Najeriya Birgediya Sani Usman Kuka-Sheka, ya ce an kashe gaba-daya 'yan Boko Haram din da suka kai harin.

Harin dai ya faru ne a yankin Jiddari Polo, wata unguwa da ke wajen Maiduguri, a daidai lokacin da mutane ke shirin buda-baki

Mazauna yankin sun ce amon bindigogi ya barke har tsawon kimanin sa'a guda.

Shin kun dauki rundunar 'yan sandan Najeriya a matsayin abokai?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel