Mutum 1 ya mutu, 18 sun jikkata a wani mummunan hatsarin mota

Mutum 1 ya mutu, 18 sun jikkata a wani mummunan hatsarin mota

- Akalla mutum 1 ya mutu a yayin da wasu mutane 18 suka jikkata a wani hadarin mota da ya afku tsakanin wasu mutane 19 a babban hanyar Lagos-Ibadan.

- Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne a daidai karfe 8:30 na dare kusa da kauyen Guru Maharaji a jihar Ibadan, tsakanin motoci guda 3.

Shaidu sun ce wani babban motar man fetur mai lambar rajista EPE 88 XT ya lallace yayin da ya kaure bas din Mazda mai lambar WWD 772 XA da kuma motar Toyota Camry mai lambar rajista LSR 349 SF

NAIJ.com ta samu labarin cewa a yayin da ya ke tabbatar da faruwan hadarin, kwamandar Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) na yankin, Mr. Yusuf Salami ya ce, hadarin ya faru ne sakamakon kokarin shan-kai tare da lalacewan injin wanda ya hada da gazawar birkin mota.

Mutum 1 ya mutu, 18 sun jikkata a wani mummunan hatsarin mota

Mutum 1 ya mutu, 18 sun jikkata a wani mummunan hatsarin mota

Ya ce wani balagaggen namiji ya rasa ransa, karawa an tafi da gawarsa zuwa dakin ajiyar gawa dake Asibitin Adeoyo.

Salami ya ce sauran mutane 18 da suka jikkata an tafi da su zuwa Asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan don a masu magani.

Ya kuma ce a cikin wadanda suka jikkata sun hadda da wasu kananan yara guda 4.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel