Kwarmato: Gwamnati ta fara biyan mutane 20 miliyoyin Nairori

Kwarmato: Gwamnati ta fara biyan mutane 20 miliyoyin Nairori

- A karon farko gwamnatin Najeriya ta biya masu tona asirin barayin gwamnati, inda ta biya mutum 20 naira miliyan 375,875,000.

- Kawo yanzu, gwamnatin ta kwato Naira biliyan 11,635,000,000 a sakamakon wannan tsari da aka fito da shi a watan Disamban bara.

Ministar Kudi ta Najeriya Kemi Adeosun ta ce: "Wannan shi ne karon farko da muka biya wadannan kudaden a karkashin shirin nan na masu tona asirin barayin gwamnati, kuma yana nuna jajircewar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari game da cika alkawurra... ".

Ta kara da cewa "tsarin muhimmin bangare ne na yaki da cin hanci".

NAIJ.com ta samu labarin cewa tun farkon shekarar nan, jami'an tsaroa a Najeriya sun bankado makudan kudaden da ake zargin an boye a wurare daban-daban.

Kwarmato: Gwamnati ta fara biyan mutane 20 miliyoyin Nairori

Kwarmato: Gwamnati ta fara biyan mutane 20 miliyoyin Nairori

A daya bangaren, yakin ya samu koma baya. Hukumar EFCC ta kama wasu mutanen da suka sanar da ita bayanan da basu samar da biyan bukata ba.

Hukumar ta kai farmaki wasu wurare domin gano kudaden da suka ce wai an boye su a wasu wurare. Amma samamen bai samar da komai ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel