Saudiyya na da hannu a kaimana hari, kuma zamuyi maganin ta - Kasar Iran

Saudiyya na da hannu a kaimana hari, kuma zamuyi maganin ta - Kasar Iran

- Askarawan juyin-juya-halin ƙasar Iran sun zargi ƙasashen Saudiyya da Amurka da hannu a harin da aka kai wa majalisar dokokin ƙasar da kuma hubbaren jagoran juyin-juya-halin Iran Ayatollah Khomeini.

- Kasar Saudiyya ta musanta zargin hannu kan duk wani abu da ya shafi harin da ƙungiyar IS ta ce ita ke da alhakin kai wa.

Da yake taya alhininsa kan mutum 12 da suka mutu a harin, shugaban Amurka Donald Trump, ya yi kashedin cewa duk ƙasar da ke mara wa ta'addanci baya, ita ma za ta faɗa cikin hatsarin ta'asar 'yan ta'addan.

NAIJ.com ta samu labarin cewa kasar Iran din ta ce maharan da suka hallaka mutum 12 tare da jikkata wasu da dama a Tehran babban birnin kasar Iraniyawa ne da suka shiga ƙungiyar IS da ke kiran kanta daular musulunci.

Yan harin ƙunar-bakin-wake ne dai suka kai hari a ginin majalisar dokoki da kuma a hubbaren jagoran juyin-juya-halin Islama na Iran Ayatollah Khomeini.

Saudiyya na da hannu a kaimana hari, kuma zamuyi maganin ta - Kasar Iran

Saudiyya na da hannu a kaimana hari, kuma zamuyi maganin ta - Kasar Iran

Kungiyar IS ta ce ita ce ke da alhakin kai harin, ta kuma yi barazanar cewa wannan shi ne mafarin hare haren da za ta rika kai wa.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi Allah wadai kai hare haren.

Duka maharan dai sun mutu, yayin da aka cafke wasu mutum biyar da aka yi amanna suna shirin kai hari na uku, in ji hukumomi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel