Siriki ya danƙara ma sirikarsa ciki, ya sallami matarsa

Siriki ya danƙara ma sirikarsa ciki, ya sallami matarsa

- Wata mata mai suna Queen Stephen ta nemi wata kotu ta raba aurenta

- Matar tace mijin nata ya dankara ma kanwarta ciki

Wata mata mai suna Queen Stephen ta nemi wata kotun gargajiya dake garin Legas data raba aurenta da mijinta, da suka kwashe shekaru 12 ana tare.

Daily Trust ta ruwaito matar tana bayyana ma kotun cewar mijinta mai suna Francis Stephen,uban yayanta guda hudu ya maka ma kanwarta ciki a shekarar 2016.

KU KARANTA: Ba zan yarda Kwankwaso ya haye ma Ganduje da Abdullahi Abbas ba – Musa Iliyasu

“ A lokacin dana haihu, sai na dauko kanwata ta zauna dani domin taimaka min wajen aikin jego, daga nan ne fa maigidana ya zagaya ya dankara mata ciki, kuma ita ma ta tabbatar min shi ne yayi mata ciki.” Inji matar.

Siriki ya danƙara ma sirikarsa ciki, ya sallami matarsa

Kotun

Matar ta zargi mijinta da watsar mata da kayanta, tare da korarta zuwa kauyensu, a cewarsa wai baya son zaman aure da ita, sa’annan tace mijin mashayin giya ne:

“Wannan mutumin yana barazana ga rayuwa na, yayi barazanar babbaka ni da wuta, har dutsen guga ya taba nana min da nufin kona ni. Haka dai mutumin ya cigaba da ci min mutunci. Don haka nake son a raba auren mu.” Inji ta

A nasa barayin, mijin matar ya zargi matar da yawon banza, inda ma a cewarsa yace har ciki tayi a waje tare da wani mutum, amma sai ta zubar da shi, inji majiyar NAIJ.com.

“Saurayin ta da kansa ya bayyana min cewar shi yayi mata ciki, ind a yace sau biyar ya kwanta da ita, amam ita kuma ta musa tace sau hudu ne, har ma Faston ta take kwanciya” inji Mijin yayin dayake bayani ga kotu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaki iya auren rantsuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel