Ministan cikin gida, Dambazau ya tofa albarkacin bakinsa kan barazanar da akayiwa Igbo

Ministan cikin gida, Dambazau ya tofa albarkacin bakinsa kan barazanar da akayiwa Igbo

- Abdulrahman Dambazau, ya bukaci ‘yan Najeriya da su zauna lafiya sannan kuma su guji duk wani abu da zai haddasa rashin jituwa

- Ya yi Allah wadai da irin wannan kira sannan kuma ya bayyana hakan a matsayin aiki mara kyau

- Ya ce gwamnatin tarayya zata dauki kwakkwaran mataki a kan duk mutumi ko kungiya da ya saba ma hakkin sauran ‘yan kasa

A ranar Alhamis, 7 ga watan Yuni, Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau, ya bukaci ‘yan Najeriya da su zauna lafiya sannan kuma su guji duk wani abu da zai haddasa rashin jituwa.

Ministan cikin ya yi kiran ne a cikin wani jawabi daga hannun sakataren sa, Ehisienmen Osaigbovo, a Abuja, a kokarin maida martani ga kiran da kungiyoyin matasan Arewa sukayi ga ‘yan kabilar na su bar yankin Arewa.

Ya yi Allah wadai da irin wannan kira sannan kuma ya bayyana hakan a matsayin aiki mara kyau.

Ministan cikin gida, Dambazau ya tofa albarkacin bakinsa kan barazanar da akayiwa Igbo

Ministan cikin gida, Dambazau ya tofa albarkacin bakinsa kan barazanar da akayiwa Igbo

Mista Dambazau ya ce gwamnatin tarayya zata dauki kwakkwaran mataki a kan duk mutumi ko kungiya da ya saba ma hakkin sauran ‘yan kasa.

KU KARANTA KUMA: Matashiya ta mutu sa’o’I 24 bayan ta fada ma kawarta cewa ta ji a jikinta zata mutu

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su koma kan harkokinsu na yau da kullun ba tare da ko wani tsoro ba.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya zata tabbatar da cewan ‘yan kasa na gudanar da ayyukansu cikin yanci ba tare da cin zarafi ba.

Ya shawarci kungiyoyin kasar daban-daban da su janye daga kiyayen junansu da tayar da fitina da rashin jituwa.

Ya yi kira gare su da su yi koyi da koyi da kyawawan koyarwan addinai da al’addu wanda ya karfafa kyakyawan alaka da makwabta, hadin kan kasa, amana da kuma soyayyar juna.

Mista Dambazau ya shawarci matasa da karda su yarda ayi amfani da su ggurin tayar da zaune tsaye a kasar. Cewar Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN)

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com, 'Yan Najeriya sun yi kewan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel