EFCC tayi wani sabon wawan kamu, ta maka mutane 3 kotu kan satar kudi

EFCC tayi wani sabon wawan kamu, ta maka mutane 3 kotu kan satar kudi

- Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC ta gurfanar da wasu mutane uku a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja, kan zarge-zarge 13 da suka hada da, hada kai da kuma karbar kudi ta hanyar yin karya.

- Wadanda ake zargin sun hada da, Esther Onukaogu, Jennifer Ebenuwa da kuma Joshua Onukaogu.

- Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren,ya bayyana haka a wata sanarwa da yafitar yau Talata.

Yace Onukaogu taci amanar ofishinta, lokacin da take aiki da kamfanin Soft Alliance, wani kamfanin kwararru dakewa ofishin babban mai binciken kudi na kasa aiki kan Sabon tsarin nan na tantancewa da kuma biyan ma’aikata dake kira IPPIS a turance, tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015.

NAIJ.com ta samu labarin cewa yace matar da ake zargi ta saka sunanta dana yan uwanta a cikin tsarin na IPPIS, karkashin ma’aikatar ilimi da kuma ma’aikatar aiyuka domin su rika karbar albashi daga gwamnatin tarayya.

EFCC tayi wani sabon wawan kamu, ta maka mutane 3 kotu kan satar kudi

EFCC tayi wani sabon wawan kamu, ta maka mutane 3 kotu kan satar kudi

Uwujaren yace Onukaogu da sauran wadanda ake kara sun karbi albashi daga ma’aikatun na tsawon shekaru uku da yakai naira miliyan 9, kafin dubunsu ta cika.

Wadanda ake karar sun musalta dukkanin zarge-zargen da akeyi musu,an kuma bada belinsu kan kudi naira miliyan 5.

Mutanen zasu cigaba da zama a hannun hukumar ta EFCC, har sai sun cika sharudan belin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel