Ko ba Kannywood tauraruwata zata cigaba da haskawa - Rahma Sadau

Ko ba Kannywood tauraruwata zata cigaba da haskawa - Rahma Sadau

Rahma Sadau fitacciyar Jarumar da kungiyar shirya finafinan Hausa ta MOPPAN ta haramtawa sake fitowa a cikin fina-finai, ta ce za ta garzaya kotu don kalubalantar korar da aka yi mata.

NAIJ.com ta samu labarin cewa jarumar ta bayyana aniyarta na daukar wannan mataki ne a shafinta na sada zumunta da muhawara na Facebook, a inda ta lika wani takaitaccen sakon maratani ga korar ta na mai cewa:

“Zan yi shari’a da Kannywood”,

Sannan Kuma ta a rubuta cikin harshen Ingilishi, ”

”Shin Kannywood ce kadai inda ake shirin fim?"

Ko ba Kannywood tauraruwata zata cigaba da haskawa - Rahma Sadau

Ko ba Kannywood tauraruwata zata cigaba da haskawa - Rahma Sadau

A wani labarin kuma, sananniyar ‘Yar wasan Hausa Film Nafisat Abdullahi ta mayar da martani akan kalaman da korarriyar jarumar nan Rahama Sadau tayi akan ‘yan Matan Hausa Film, inda ta zarge su da hassada da girman Kai.

Nafisa Abdullahi ta bayyana cewar, kalaman da Rahama Sadau ta keyi sambatu ne kawai na jin haushin korar da akayi mata a Masana’antar film, amma duk da haka ya kamata Rahamar ta sani cewar Matan Hausa Film sun wuce da tunanin ta, saboda Mata ne wayayyu masu ilimi wadanda suka fahimci rayuwa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel