An kashe 'yan Boko Haram da suka kai hari Maiduguri – Inji Rundunar Sojoji

An kashe 'yan Boko Haram da suka kai hari Maiduguri – Inji Rundunar Sojoji

- Rundunar sojin Najeriya tace ta kashe 'yan Boko Haram da suka kai hari a garin Maiduguri a ranar Laraba

- Daraktan yada labaran sojin kasar, ya ce sojojin sun samu galaba a kan maharani

- Daraktan ya tabbatar da karfafa tsaurara matakan tsaro tare da kara dakaru a yankin

- Rikicin Boko Haram da ya soma a shekarar 2009 ya yi sanadi rayuka 100,000

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe daukacin mayakan Boko Haram da suka kaddamar da munanan hare-hare a wasu sassan birnin Maiduguri a daren ranar Laraba, 7 ga watan Yuni.

Daraktan yada labaran sojin kasar, Brigadier Janar Sani Usman Kukasheka, ya ce maharan sun kaddamar da harin ne a yankin Jiddari Polo da ke cikin garin, amma kuma sojojin sun samu galaba a kan su.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Sani Usman ya ce da farko mazauna yankin sun shirya tserewa daga gidajensu amma yanzu komai ya lafa.

Jami'in ya kuma tabbatar da karfafa tsaurara matakan tsaro tare da kara dakaru a yankin don hana barazanar irin wannan hari na bazata a nan gaba.

KU KARANTA: Mutane 8 sun hallaka, 37 sun jikkata a harin Boko Haram na Jiddari Polo

Sai dai babu wani karin haske kan adadin wadanda suka mutu ko Jikkata.

An kashe 'yan Boko Haram da suka kai hari Maiduguri – Inji Rundunar Sojoji

Sojoji masu fafatawa da kungiyar Boko Haram

Harin ya kasance irinsa na farko da mayakan Boko Haram ke kai wa tun bayan karbe ikon wasu yankunan da ke karkashinsu.

Rikicin Kungiyar na Jihadi da ya soma a shekarar 2009 ya yi sanadi rayuka 100,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka kubuce daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel