Ba zan yarda Kwankwaso ya haye ma Ganduje da Abdullahi Abbas ba – Musa Iliyasu

Ba zan yarda Kwankwaso ya haye ma Ganduje da Abdullahi Abbas ba – Musa Iliyasu

- Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya koma jam'iyyar APC

- Musa Iliyasu ya taba zama kwamishina a zamanin mulkin Malam Ibrahim Shekarau

Tsohon kwamishinan a jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso yace bai shigo cikin jam’iyyar APC da nufin rikici da tsohon gwamnan jihar Rabiu Kwankwaso ba, inji rahoton Daily Trust.

Musa Iliyasu ya taba zama kwamishina a zamanin mulkin Malam Ibrahim Shekarau, kuma a juma’ar satin data gabata ne yayi wankan tsarki daga jam’iyyar PDP zuwa APC a garin Madobi.

KU KARANTA: Shanun makiyaya sun afka azuzuwan makarantar Firamari (Hotuna)

Dayake jawabi ga majiyar NAIJ.com, Musa Iliyasu yace ya shigo jam’iyyar APC ne da nufin taimaka ma gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje wajen tafiyar da al’amuran mulki.

Ba zan yarda Kwankwaso ya haye ma Ganduje da Abdullahi Abbas ba – Musa Iliyasu

Kwankwaso

“Amma fa idan Sanata Kwankwaso yayi gigiwar haye ma gwamna Ganduje, ko shugaban jam’iyya Abdullahi Abbas, toh lallai za’a ji mu da shi.

“Amma idan Sanata Kwankwaso ya yarda da shugabancin Ganduje da na Abdullahi Abbas, toh zamu zauna lafiya da shi ba tare da wani matsala ba, kai idan ma Ganduje yace in yi ma Kwankwaso yakin neman zabe, toh zan yi masa.” Inji shi.

Daga karshe Musa Iliyasu yace ba shi da matsala da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, duk da cewa yana jam’iyyar PDP.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaka iya auran rantsuwa da mijinka

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel